Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiINEC na gudanar da aikinta ba tare da nuna son kai ba...

INEC na gudanar da aikinta ba tare da nuna son kai ba – Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) na gudanar da ayyukanta cikin adalci da bin doka, yana mai musanta zarge-zargen nuna son kai da ake yi wa hukumar.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar shugabannin Ƙungiyar Limaman Cocin Katolika ta Najeriya (CBCN) a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Ya ce INEC ba ta taɓa tsoratar da wata jam’iyya ko nuna bambanci wajen gudanar da ayyukanta ba.

Shugaban ya ƙara da cewa korafe-korafen da wasu jam’iyyun adawa ke yi kan hukumar zaɓen na iya kasancewa sakamakon rashin shiri a ɓangarensu, ba wai gazawar INEC ba.

A baya-bayan nan dai, wasu jam’iyyun adawa da ƙungiyoyi sun rika zargin INEC da nuna son kai tare da yin kira ga shugaban hukumar ya sauka daga muƙaminsa.

Sai dai Tinubu ya jaddada cewa hukumar na aiki ne bisa tanade-tanaden doka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments