Wasu ’yan bindiga sun sace ‘yan uwa uku yayin da suke rakiyar gawar mahaifiyarsu zuwa garinsu domin gudanar da jana’iza a jihar Benue.
Lamarin ya faru ne a lokacin da iyalan ke kan hanyarsu ta komawa gida da gawar mamaciyar, inda maharan suka tare su tare da yin awon gaba da mutum uku daga cikin ’yan uwan.
Rahotanni sun ce sauran mutanen da ke cikin ayarin sun tsira daga harin, yayin da maharan suka tafi da waɗanda suka sace zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Wani ɗan uwa ya bayyana cewa lamarin ya jefa iyalan cikin matsanancin baƙin ciki, domin suna cikin jimamin rasuwar mahaifiyarsu kafin wannan sabon ibtila’i ya auku.
An ce an sanar da jami’an tsaro game da harin, kuma an fara bincike tare da ƙoƙarin ceto mutanen da aka sace, yayin da ake ci gaba da farautar maharan.