Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiLabaraiDalilin da yasa gwamna Kano ya mara wa Abba Bichi baya a...

Dalilin da yasa gwamna Kano ya mara wa Abba Bichi baya a zaben 2027

Jam’iyyar APC ta ayyana Hon.Abba Bichi a matsayin ɗan takara shi kaɗai na kujerar wakilan Bichi gabanin zaɓen 2027.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana goyon bayansa ga ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bichi, Hon. Abubakar Kabir Abubakar, wanda aka fi sani da Abba Bichi, domin sake tsayawa takara a zaɓen 2027.

An bayyana hakan ne yayin taron tabbatar da ‘yan takarar jam’iyyar APC da aka gudanar a Bichi, inda aka ayyana Abba Bichi a matsayin ɗan takara shi kaɗai na kujerar majalisar wakilai.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnan ya yaba da irin ayyukan ci gaba da Hon. Abba Bichi ke gudanarwa tare da irin wakilcin da yake yi wa al’ummar mazabarsa.

Gwamna Abba ya ce tun daga shekarar 2023 yake fatan yin aiki tare da ɗan majalisar domin ciyar da Bichi da jihar Kano gaba.

Ya kuma ce gudunmawar da Abba Bichi ke bayarwa wajen tallafawa matasa da raya al’umma na ci gaba da kawo sauyi mai kyau a yankin.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments