Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiLabaraiKalubalen da ke gaban gwamnoni masu neman wa’adi na biyu a APC

Kalubalen da ke gaban gwamnoni masu neman wa’adi na biyu a APC

Alamu na nuna cewa akalla gwamnoni biyar na jam’iyyar APC za su fuskanci tsananin ƙalubal wajen neman tikitin tsayawa takara karo na biyu a zaɓen 2027.

Alamu na nuna cewa akalla gwamnoni biyar na jam’iyyar APC za su fuskanci tsananin ƙalubal wajen neman tikitin tsayawa takara karo na biyu a zaɓen 2027.

Wannan na zuwa ne duk da cewa jam’iyyar APC na ƙoƙarin amfani da tsarin maslaha domin fidda ‘yan takara a wasu jihohi.

Rahotanni sun nuna cewa wasu gwamnoni masu neman wa’adi na biyu da kuma waɗanda ke son miƙa mulki ga waɗanda suke goyon baya, suna fuskantar matsaloli daga cikin jam’iyyar.

Sai dai wasu gwamnoni 13 ana sa ran za su samu tikitin jam’iyyar ba tare da hamayya ba, saboda babu wanda ya nuna sha’awar ƙalubalantarsu.

Daga cikin waɗannan gwamnoni akwai: Umar Namadi, Uba Sani, Abba Kabir Yusuf, Dikko Umaru Radda, Nasir Idris da sauran su.

Rahotanni sun ce jihar Kwara ce ke da mafi yawan masu neman takarar gwamna, inda mutum 15 ke neman tikitin jam’iyyar. Sauran jihohin da ake da yawan masu neman takara sun haɗa da Adamawa, Oyo, Yobe, Bauchi, Nasarawa, Taraba da Gombe.

A jihar Benue kuwa, rikicin siyasa tsakanin gwamna Hyacinth Alia da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, na iya shafar damar gwamnan wajen sake samun nasara.

A Taraba ma akwai rashin jituwa, inda wasu ‘yan takara uku suka ƙi amincewa da tsarin maslaha da gwamnan jihar ke son amfani da shi.

A jihar Plateau, wani tsohon jami’in soja mai ritaya, Jan Bida, ya sayi fom ɗin takarar gwamna duk da batun tsarin maslaha.

A Ebonyi kuma, ana zargin akwai saɓani tsakanin Ministan Ayyuka, David Umahi da gwamnan jihar Francis Nwifuru kan yadda ake tafiyar da harkokin jam’iyyar.
Haka kuma a Jigawa, ana rade-radin samun rashin jituwa tsakanin tsohon gwamnan jihar kuma tsohon Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar da magajinsa Umar Namadi, musamman kan iko da shugabancin jam’iyyar APC a jihar.

A Adamawa kuwa, ana ganin akwai takun saka tsakanin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da wani babban jami’in tsaro daga jihar kan wanda zai samu tikitin gwamna a jam’iyyar.

A Yobe kuwa, masu neman takarar gwamna guda shida sun ƙi amincewa da batun ayyana tsohon Sakataren Gwamnatin jihar, Baba Mallam Wali, a matsayin ɗan takarar maslaha.

A Gombe ma, gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya zaɓi Jamilu Isyaku Gwamna a matsayin wanda yake so ya gaje shi, lamarin da ya jawo koke daga wasu masu neman takara ciki har da Isa Ali Pantami.

Wani masanin siyasa, Jide Ojo, ya shawarci APC da ta bari a gudanar da zaɓen fidda gwani kai tsaye a jihohin da ake samun rashin jituwa maimakon tilasta tsarin maslaha.

Ya ce tilasta tsarin maslaha na iya ƙara rikici a cikin jam’iyyar tare da rage ƙarfin APC a wasu jihohi.

A cewarsa, ya kamata a bai wa gwamnoni da sauran masu neman takara damar gwada farin jininsu ta hanyar zaɓe mai gaskiya da adalci.

Rahotanni sun kuma nuna cewa APC na ci gaba da tantance masu neman takara, yayin da kwamitin sauraron ƙorafe-ƙorafe zai fara aiki kafin a fitar da jerin sunayen waɗanda suka samu nasarar tsallake tantancewa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments