Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiFintiri da Kwacham na shirin fafatawa a kujerar Sanatan Adamawa ta Arewa

Fintiri da Kwacham na shirin fafatawa a kujerar Sanatan Adamawa ta Arewa

Alamu sun nuna cewa ana dab da shiga wata babbar fafatawa ta siyasa tsakanin gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, da wani hamshakin ɗan kasuwa da ya koma siyasa, Abdulrahman Kwacham, kan kujerar Sanatan Adamawa ta Arewa a zaɓen 2027.

Alamu sun nuna cewa ana dab da shiga wata babbar fafatawa ta siyasa tsakanin gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, da wani hamshakin ɗan kasuwa da ya koma siyasa, Abdulrahman Kwacham, kan kujerar Sanatan Adamawa ta Arewa a zaɓen 2027.

Magoya baya da abokan siyasar Kwacham sun cika tsohon garin kasuwanci na Mubi a ranar Alhamis domin tarbarsa, lamarin da ya sa garin ya tsaya cik na ɗan lokaci. Wannan taro ya nuna shirinsa na shiga takarar Sanata domin wakiltar yankin a majalisa mai zuwa.

Da yake jawabi a wajen taron, Abubakar Inuwa, tsohon mataimakin shugaban kula da shige da fice, ya ce Kwacham ya taka rawar gani sosai wajen ci gaban Mubi. Ya bayyana irin gudummawar da ya bayar wajen samar da ayyukan yi ga matasa a fannoni daban-daban na gwamnati da masu zaman kansu.

Inuwa ya ce al’ummar yankin sun dade suna kira gare shi ya fito takara, suna ganin salon jagorancinsa mai amfani zai taimaka wajen kawo ci gaba da rabon arzikin ƙasa ga yankin.

Ya kuma tabbatar da cewa sun kai ziyara ga Sarkin Mubi, Alhaji Abubakar Isah Ahmadu ne domin neman albarka kafin fara wannan tafiya ta siyasa.

A cewarsa, hanya mafi dacewa wajen warware rikicin burin takarar tsakanin Kwacham da Fintiri ita ce tattaunawa da fahimtar juna; in ba haka ba, za a bar jam’iyya ta warware lamarin a zaɓen fidda gwani.

A lokaci guda kuma, wasu kungiyoyin matasa, ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa daga ƙananan hukumomi biyar na Adamawa ta Arewa sun gudanar da gangamin goyon baya ga gwamna Fintiri domin ya tsaya takarar wannan kujera.

A wajen gangamin da aka yi a Mubi ranar Asabar, sun bayyana Fintiri a matsayin wanda ya fi dacewa da kujerar, suna mai cewa shi ne “magajin halas” na wannan mukami a 2027.

Manyan jagororin al’umma da suka halarci taron, ciki har da kwamishinan ayyuka da samar da makamashi, Suleiman Mohammed, da mai ba shugaban ƙaramar hukumar Mubi ta Arewa shawara, Adamu Risku, sun ce wannan kira yana nufin a ci gaba da samun ci gaba a yankin.

Ƙarfafa goyon bayan Fintiri ya ƙaru bayan da ya koma jam’iyyar APC, matakin da masana siyasa ke ganin ya haɗa kan tsarin siyasar yankin.

Magoya bayansa na ganin cewa idan ya shiga majalisar dattawa, zai taimaka wajen tabbatar da cewa Adamawa ta Arewa na ci gaba da samun kulawa a matakin ƙasa.

Sai dai har yanzu gwamnan bai bayyana aniyarsa a hukumance ba, domin yana mai da hankali kan kammala ayyukan wa’adinsa na biyu, duk da cewa photuna da tallace-tallacen “Fintiri for Senate” suna ta yaɗuwa a kafafen sada zumunta.

Dukkaninsu, Fintiri da Kwacham, mambobi ne na jam’iyyar APC mai mulki, kuma kowanne bangare na ganin ɗan takararsu ya fi cancanta. Sai dai masana siyasa na ganin cewa lokaci ne kawai zai bayyana wanda zai yi nasara a ƙarshe.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments