Jam’iyyar ADC ta sanar da ranar 12 ga watan Mayun 2026 a matsayin ranar rantsar da sabbin shugabannin jihohi da shugabannin jam’iyya da aka zaɓa a faɗin ƙasar.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ya fitar, ADC ta taya waɗanda aka zaɓa murna kan yadda aka gudanar da zaɓukan cikin lumana, tare da bayyana hakan a matsayin hujjar jajircewar jam’iyyar wajen bin tsarin dimokuraɗiyya, gaskiya da bin doka.
Jam’iyyar ta ce an gudanar da zaɓukan ne bisa kundin tsarin mulkinta da dokokin da suka dace, tare da yaba wa mambobi da masu ruwa da tsaki kan yadda aka gudanar da tsarin cikin tsari da ladabi.
Ta kuma bayyana cewa za a iya sauya ranar rantsarwar idan akwai buƙata, bisa shawarar kwamitin gudanarwa na ƙasa.
ADC ta buƙaci sabbin shugabannin da aka zaɓa da su kasance masu biyayya ga manufofin jam’iyyar, tare da aiki kafada da kafada da shugabanta na ƙasa, David Mark, domin ƙarfafa jam’iyyar a faɗin ƙasa.
Ta jaddada cewa aikin da ke gabansu yana buƙatar haɗin kai, ladabi da jajircewa domin gina jam’iyya mai ƙarfi da za ta samar da siyasa mai inganci ga ‘yan Najeriya.
Jam’iyyar ta kuma nuna kwarin gwiwa cewa ƙarƙashin sabbin shugabannin jihohi, za ta ci gaba da faɗaɗa tsarinta tare da ƙara kusanci da jama’a a duk faɗin ƙasar.
A wani ɓangare kuma, shugaban INEC, Joash Amupitan, ya gargadi jam’iyyar kan ci gaba da gudanar da tarurrukan ta, yana mai cewa hakan na iya saba umarnin kotu.
Sai dai ADC ta mayar da martani cewa za ta ci gaba da shirye-shiryenta, tana mai zargin INEC da karkatar da fassarar hukuncin kotu da kuma ƙoƙarin dakatar da ayyukan halal na jam’iyyar.
Ta ƙara da cewa matsalolin cikin gida ba sa hana gudanar da ayyukan dimokuraɗiyya, tana mai jaddada cewa za ta ci gaba da bin doka da kuma tsarin dimokuraɗiyya yadda ya dace.