Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da aka yanke wa hukuncin kisa bisa zargin batanci, ya shigar da kara yana neman a mayar da shi Kano daga gidan yarin Kuje a Abuja.
A cikin wani korafin da ya gabatar a gaban Kotun Daukaka Kara a Kano, mai dauke da kwanan wata 3 ga Afrilu, 2026, malamin ya ce sauya masa wuri zuwa Abuja ya hana shi samun muhimman takardun da yake bukata domin daukaka karar da ya shigar.
Rahotanni sun nuna cewa takardun, wadanda suka kunshi sama da shafuka 5,000 da suka kunshi bayanan shari’a da hujjojin da ya ce yana da su, suna gidan yarin Kurmawa lokacin da aka mayar da shi Kuje.
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya jaddada cewa yana bukatar tabbatar da cikakkun takardunsa kafin a ci gaba da sauraron shari’ar da ake.