Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiYanzu za mu fara kai hare-hare bayan na ramuwar gayya – Iran

Yanzu za mu fara kai hare-hare bayan na ramuwar gayya – Iran

Iran ta sanar da cewa yanzu za ta fara kai hare-haren mayar da martani.

Iran ta bayyana cewa ta kawo ƙarshen salon hare-haren mayar da martani, inda ta ce daga yanzu za ta fara kai hare-hare ne kai tsaye maimakon ramuwar gayya.

Mai magana da yawun hedikwatar rundunar sojin Khatam al-Anbiya, Ebrahim Zolfaqari, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce “Iran ta kawo ƙarshen salon hare-haren mayar da martani, yanzu luguden wuta ne kawai za ta riƙa yi.”

Iran ta kuma bayyana cewa ba za ta bari ko lita ɗaya na mai ya wuce ta mashigar Mashigar Hormuz ba domin isa ga Amurka da Isra’ila da kuma abokan hulɗarsu ba.

Zolfaqari ya ƙara da cewa duk wani jirgin ruwa ko tankar mai da ke kan hanyar zuwa Amurka ko Isra’ila ko abokan hulɗarsu za a kai musu hari.

Haka kuma ya ce a shirya ganin farashin gangar mai ya kai dala 200, yana mai cewa farashin mai yana da alaƙa da tsaron yankin da ya zargi waɗannan ƙasashe da lalatawa.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments