Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiRayuwar baƙin haure na cikin haɗari sanadiyyar azabtarwar Libya – MDD

Rayuwar baƙin haure na cikin haɗari sanadiyyar azabtarwar Libya – MDD

MDD ta bayyana cewa rayuwar bakin haure na cikin hadari

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya, ya nuna cewa rayuwar baƙin haure, ciki har da ƙananan yara na cikin haɗarin gaske, sakamakon azabtarwa, bautarwa, fyaɗe da suke fuskanta a Libya, wanda ya yi kira da a dakatar da shirin tsugunar da ƴan ciranin da ake jibgewa a ƙasar har sai an tabbatar da ƴancin dan adam.

Libya ta zama hanyar jigilar ƴan cirani da ke tserewa rikici da talauci zuwa Turai ta hanyar Bahar Rum tun bayan kifar da gwamnatin Muammar Gaddafi a shekarar 2011, bayan boren da ake zargin NATO ce ta haddasa.

A cikin ƴan shekarun nan, Ƙungiyar Tarayyar Turai ta bayar da tallafi tare da horar da masu tsaron gabar tekun Libya, waɗanda aka ɗorawa alhakin ajiye ƴan ciranin da aka samu zuwa cibiyoyin da aka tanadar musu.

Wani rahoton Ofishin Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya ce masu safarar mutane na kama ƴan cirani ko kuma sace su waɗanda galibi suna da alaƙa da hukumomin Libya da ƙungiyoyin masu aikata laifuka a ƙasashen waje.

Mai magana da yawun Ofishin Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, Thameen Al-Kheetan yayin wani taron manema labarai a Geneva, ya ce waɗannan baƙi dai ana raba su da iyalansu, sannan a mayar da su wuraren da aka keɓe ba tare da bin ƙa’ida ba, wanda hakan ke nufin tsarewa ba bisa ƙa’ida ba.

Hukumomin Libya a baya sun musanta duk wani cin zarafi da ake zargin suna tafkawa kan bakin haure.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments