Tsohon Sanatan Kogi, Dino Melaye, ya ce ya biya kuɗin karatunsa ta hanyar kiwon awaki da ya fara tun yana ɗan shekara 12.
Melaye, jigo a jam’iyyar ADC, ya bayyana hakan ne a shirin KaaTruths podcast ranar Asabar.
Ya ce ya sayi akuya ta farko yana da shekara 12, sannan ya riƙa sayar da ’ya’yanta domin biyan kuɗin makarantar sakandare, WAEC da JAMB.
Ya ƙara da cewa kuɗin kiwon awakin sun taimaka masa wajen biyan shekarunsa biyu na farko a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU).
Melaye ya ce tun yana shekara 18 ya fara saka hannun jari a ƙasashen waje, inda daga baya ya shiga kasuwar kuɗi da sayen hannun jari a kamfanoni irin su Apple, Microsoft, Uber da Zoom.
Ya ce wasu abokansa sun yi masa dariya kan wasu daga cikin jarinsa, amma daga baya ya samu riba mai yawa.
Tsohon sanatan ya kuma musanta cewa dukiyarsa ta samo asali ne daga siyasa, yana mai cewa tun bayan barin majalisar gwamnati a 2019, matsayinsa na kuɗi bai ragu ba.