Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiFicewar baƙin fata daga Afirka ta Kudu ya jawo ƙarancin ma’aikata a...

Ficewar baƙin fata daga Afirka ta Kudu ya jawo ƙarancin ma’aikata a kasar

Afirka ta Kudu na fuskantar matsalar ƙarancin ma’aikata bayan da rahotanni suka nuna cewa sama da baƙi 160,000 sun bar ƙasar sakamakon hare-haren ƙyamar baƙi, tsaurara matakan shige da fice da kuma rashin tsaro.

Rahotanni sun nuna cewa ficewar baƙin ta fara yin tasiri a muhimman fannoni kamar noma, gine-gine, aikin gida da masana’antu, inda masu ɗaukar ma’aikata ke fuskantar matsalar samun waɗanda za su maye gurbin waɗanda suka bar ƙasar.

Manoma da masu masana’antu sun bayyana cewa ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan ƙasashen waje na iya rage yawan amfanin da ake samarwa, yayin da wasu ƙungiyoyin ƙwadago ke zargin wasu kamfanoni da fifita baƙi saboda ƙarancin albashin da ake biyansu.

A halin yanzu, gwamnatin Afirka ta Kudu na ƙoƙarin nemo mafita da za ta daidaita tsakanin samar da guraben ayyukan yi ga ‘yan ƙasar da kuma biyan buƙatun sassan tattalin arziki da suka dogara da ma’aikatan ƙasashen waje.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments