Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiSama da mutum 100 na hannun ‘yan bindiga – shugaban ƙaramar hukuma...

Sama da mutum 100 na hannun ‘yan bindiga – shugaban ƙaramar hukuma a Sokoto

Shugaban karamar hukumar Wurno a jihar Sokoto ya bayyana fargaba a kan yadda jama'a ke barin gidajensu sakamakon ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga.

Shugaban karamar hukumar Wurno a jihar Sokoto ya bayyana fargaba a kan yadda jama’a ke barin gidajensu sakamakon ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga.

Ya ce lamarin ya zama babban abin damuwa ga jama’a, gwamnatin jiha da ta tarayya, da kuma jami’an tsaro, yana mai cewa hare-haren yanzu sun zama kusan kullum a wasu sassan ƙaramar hukumar.

“Mutane ba sa iya barci da kwanciyar hankali,” in ji shi yayin da yake magana da manema labarai a Sokoto.

Shugaban ya koka cewa an rasa rayuka da dukiyoyi da dama sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a ‘yan shekarun nan, inda ya ƙara da cewa sama da mutum 100 na hannun ‘yan bindiga a yankin a halin yanzu.

Ya ce dubban mutane na zuwa garin Achida kowane yammaci domin kwana, sannan su koma garuruwansu da rana.

“Suna kwana a makarantu da sauran wuraren da suka samu. Ka yi tunanin irin damuwar tunani da ta zuciya da suke fuskanta kullum,” in ji shi.

Sadiq-Achida ya kuma nuna damuwa kan masu ba ‘yan bindiga bayanai daga cikin al’umma, amma ya ce jama’a sun fara taimakawa jami’an tsaro da sahihan bayanai tare da kafa ƙungiyoyin sa-kai.

Ya ce ‘yan bindiga kan tare manyan hanyoyi da dare, musamman a ranakun kasuwa a Achida da Goronyo.

Yayin da ya yaba wa gwamnan jihar, Ahmed Aliyu, kan ƙoƙarin inganta tsaro, shugaban ya buƙaci a ƙara ɗaukar matakan gaggawa, ciki har da kafa sansanin soja a Achida.

Haka kuma ya roƙi a ƙirƙiri ƙarin ofisoshin ‘yan sanda a Achida, Kwargaba, Chacho da sauran yankuna masu haɗari

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments