Wani matashi mai shekara 25, Ibrahim Mbaya, wanda aka fi sani da “Ibee”, kuma wanda ya kammala karatu a Jami’ar Jos, ya rasu bayan da wasu matasa suka lakada masa duka bisa zargin satar waya.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a wani gida da ke wajen harabar jami’ar, bayan unguwar City of David da ke kan titin Ring Road a Jos. Wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna yadda ake dukansa da katako da bulala har sai da ya rasa ransa.
Rahotanni sun ce marigayin ya halarci wani taro a jami’ar kafin ya kwana a gidan wani abokinsa saboda dare ya yi. Washegari, abokan nasa sun yi zargin cewa wayar iPhone 12 ta ɓace, kuma suka zarge shi da satar wayar, inda suka yi masa dukan da ya kai ga mutuwarsa maimakon kai rahoto ga jami’an tsaro.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato ta tabbatar da kama mutane uku da ake zargi da hannu a kisan. Ta ce bincike ya nuna cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka kama ya fito a bidiyon da ke yawo yana bugun marigayin da wani babban katako.
’Yan sandan sun yi Allah wadai da abin da suka bayyana a matsayin ɗaukar doka a hannu, tare da jaddada cewa duk wanda ake zargi da aikata laifi yana da haƙƙin samun shari’a bisa doka. Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin tabbatar da an hukunta duk masu hannu a lamarin.