Sunday, October 18, 2026
HomeKasuwanciFadar shugaban ƙasa ta ce farashin shinkafa ya yi kwasha-kwasha a wasu...

Fadar shugaban ƙasa ta ce farashin shinkafa ya yi kwasha-kwasha a wasu wurare a Najeriya

Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta bayyana cewa farashin kayan abinci ya ragu a ƙasar, inda ta ce ana sayar da buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 kan ƙasa da Naira 50,000 a wasu wurare, bayan da a baya farashinsa ya kai Naira 120,000.

Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a, 16 ga Oktoba, 2026, kamar yadda jaridar Aminiya ta Daily Trust ta ruwaito.

Onanuga ya ce a garinsu ana sayar da buhun shinkafa kan Naira 45,000, inda ya buƙaci masu sukar manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu su riƙa ziyartar kasuwanni domin su ga sauyin farashin kayan abinci.

Ya kuma zargi wasu masu gabatar da shirye-shiryen talabijin da ci gaba da yaɗa ra’ayin ’yan adawa cewa tattalin arzikin Najeriya bai samu wani ci gaba ba tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments