Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya musanta rahotannin da ke cewa akwai saɓani tsakaninsa da Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, yana mai bayyana cewa dangantakarsu na cike da mutunta juna da kuma haɗin kai.
Abbas ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wani taro, inda ya ce jita-jitar da ake yaɗawa game da rikici a tsakaninsu ba ta da tushe balle makama. Ya jaddada cewa shi da gwamnan suna aiki tare domin ci gaban jihar Kaduna da kuma inganta rayuwar al’ummarta.
Ya ce babu wani sabani tsakaninsu da zai kawo cikas ga gudanar da ayyukan gwamnati ko wakilcin al’ummar Kaduna, yana mai ƙarawa da cewa suna ci gaba da tattaunawa da haɗin gwiwa kan muhimman batutuwan da suka shafi cigaban jihar.
Kakakin Majalisar ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su yi watsi da jita-jitar da ke ƙoƙarin haifar da rashin fahimta a tsakaninsu. A cewarsa, haɗin kan shugabanni yana da matuƙar muhimmanci wajen samar da ci gaba da zaman lafiya.
Rahotannin da suka yi ta yawo sun yi ikirarin cewa akwai takun-saƙa tsakanin shugabannin biyu kan wasu batutuwan siyasa a jihar Kaduna. Sai dai Abbas ya ce babu gaskiya a cikin waɗannan rahotanni, yana mai tabbatar da cewa dangantakarsu na nan daram kuma suna ci gaba da zama abokan hulɗa wajen bunƙasa jihar.